Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Tinubu Ya Rage Masu Yi Masa Rakiya Kasashen Waje Zuwa Kaso 60


NIGERIAN PRESIDENT BOLA AHMED TINUBU
NIGERIAN PRESIDENT BOLA AHMED TINUBU

Sabbin matakan za su yi tasiri ga tafiye-tafiyen manyan jami’an gwamnati da suka hada da Shugaban Kasa, Mataimakin Shugaban Kasa, da kuma Uwargidan Shugaban Kasa.

A wani gagarumin yunkuri na rage kashe-kashen kudaden gwamnati, Shugaba Bola Tinubu ya amince da rage yawan tawagar tafiye-tafiyen kasashen waje da na cikin gida zuwa kaso 60 cikin dari.

Sanarwar matakin ya fito ne daga bakin mai magana da yawun Shugaban Kasar, Ajuri Ngelale, yayin ganawa da manema labarai ranar Talata a fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

A cewar Ngelale, sabbin matakan za su yi tasiri ga tafiye-tafiyen manyan jami’an gwamnati da suka hada da Shugaban Kasa, Mataimakin Shugaban Kasa, da kuma Uwargidan Shugaban Kasa.

Don tafiye-tafiye zuwa kasashen waje, tawagar ta Shugaba Tinubu za ta kai mutum 20, wanda hakan ya ragu matuka idan aka kwatanta da tawagar da ke da mambobi 50 a baya.

Uwargidan Shugaban Kasa za ta iya daukar mutum biyar kawai, Mataimakin Shugaban Kasa kuma shima zai iya daukar biyar.

Ministoci na da mutum hudu ne kawai wanda za su kasance tare da su a balaguron kasashen waje, sannan shugabannin hukumomin gwamnati na iya daukar mutum biyu.

Manufar wadannan matakan, kamar yadda Ngelale ya bayyana, shi ne dakile almubazzaranci tare da daidaita tsarin kasafin kudin kasa.

Shugaban ya kara da cewa ya kamata jami'an gwamnati su yi kamanceceniya da tsarin kudi kamar na talakawa.

Don sanya ido kan bin wannan umarni, an ba Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume alhakin tabbatar da aiwatar da matakin, Ngelale ya shaida kakkausan gargadin Shugaban na Najeriya, inda ya bayyana cewa mutanen da aka samu sun saba wa umarnin za su fuskanci hukunci.

Haka zalika, Ngelale ya bayyana cewa Shugaban Kasar na da burin rage yawan kudaden da ake kashewa da suka shafi alawus-alawus da abubuwan da suka shafi tafiye-tafiye a cikin kasar.

Yanzu haka dai jami’an tsaro a jihohi ne za su jagoranci bada kariya ga Shugaban Kasa, Mataimakin Shugaban Kasa, da kuma Uwargidan Shugaban Kasa a lokacin da suke tafiye-tafiye a cikin Najeriya.

A karshe, Ngelale ya jaddada kudirin Shugaban Kasar na kawo karshen barnatar da kudaden gwamnati, da rage yawan kudaden da ake kashewa, da kuma tabbatar da cewa jami’an gwamnati na sarrafa dukiyar al’umma.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG