Har yanzu ba a samun tabbaci daga gwamnatin Najeriya, ba game da labari me karfi na sako ‘yan matan makarantar Chibok ba.
Rahotanni na nuni da cewa an sako ‘yan matan makarantar na Chibok wadanda ‘yan kungiyar Boko Haram, suka sace su daga makaranta fiye da shekaru biyu da suka shige.Ana harsashen cewa ‘yan mata da ake zaton cewa an sako tsakanin sittin da biyu (62) zuwa tamanin da biyu (82) ne.
Wani jami’in tsaron Najeriya, wanda ya bukaci a sakaya sunan sa ya ce yanzu haka akwai wani aikin Soja da yake gudanar dangane da wannan batun a garin Banki in da anan aka sako kashin farko na ;yan matan a shekarar da ta gabata, a iyakar Najeriya da kasar Kamaru kusa da garin Kumshe.
Facebook Forum