Tun farkon dawowarsa daga Ingila a lokacin da ya yi kiwon lafiyarsa shugaban ya fadawa ‘yan Najeriya cewa zai sake komawa nan gaba.
Ministan watsa labarai na Najeriya Alhaji Lai Mohammed, shine ya ‘kara tabbatarwa manema labarai a birnin Abuja, domin kawo karshen cece-kucen da ake ta yi akan kiwon lafiyar shugaban kasar. Inda ya ke cewa wani lokaci nan gaba shugaban zai sake ziyarar Ingila domin a duba lafiyarsa.
A yanzu dai shugaban yana ci gaba da gudanar da ayyukan ‘kasa kamar yadda ya kamata, a cewar Lai Mohammed. Ganin yadda ake ta samun cece-kuce tsakanin ‘yan ‘kasa game da kiwon lafiyar shugaban, inda wasu ke ganin ya kamata ya yi murabus wasu kuwa na ganin a tsigeshi.
Kwararre akan sha’anin dokoki Farfesa Almustapha Usiju, ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya fito fili ya bayyana yadda shugaban ‘kasa zai iya barin mulki. Na farko, shine shugaba zai iya yin kansa yayi murabus. Na biyu, shine a tsigeshi akan wani babban laifi. Na uku, rashin lafiyar da ba zai iya tashi daga ita ba. Na hudu, shine idan shugaba ya rasu.
A yanzu dai ba a kai ga wadannan abubuwa da farfesa ya zayyana ko guda ba.
Domin Karin bayani saurari cikakken rahotan Umar Faruk Musa.
Facebook Forum