Baya ga kasancewarta ranar karawa ngozomai kwarin gwuiwa ta yadda zasu gane mahimmancin wannan aikinsu na cetar rayuwa, ranar kuma rana ce ta maimaita anfanin zuwa awon ciki da faidar haihuwa a asibiti.
Ta dalilin haka ne kungiyar mata ngozomai ta Jamhuriyar Nijar ta shirya kemfen din wayar da kawunan mata a wasu asibitocin birnin Yamai kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya, ko MDD, ta bukacesu da yi ta hanyar taken ranar ta bana.
Mai magana da yawun ngozomomin tace Allah ya hadasu da mata kuma babu rabuwa sai dai mutuwa. Ke nan ngozomomi da mata masu haihuwa suke tafiya tare. Suna bukatan juna domin tsirar da rayukan jarirai tun daga ranar da aka dauki cikinsu.
Ngozoma ce take kulawa da lafiyar masu ciki tun daga ranar da aka yi ciki har zuwa haihuwa. Wannan cudanya ta zama wajibi domin a rage mace macen mata da jariransu. Yakamata suna ba juna goyon baya dari bisa dari domin su yi aikinsu yadda yakamata.
Amma da dama daga cikin mata na korafi akan rashin samun tarban da ya dace a yiwa matan da suka je asibiti walau domin awon ciki ko haihuwa. Malama Hadiza Zakari na cewa bai kamata ngozomomi su dinga kawowa mata masu juna biyu cikas ba saboda su ma mata ne. Tace ya kamayta su darajasu. Tunda sun dauki alkawarin yin aikin ngozomanci to wajibi ne su cika.
Dangane da mata masu juna biyu Hadiza ta gargedsu su yi abun da ngozomomi suka fada masu su yi. Kada su dinga taurin kai saboda domin lafiyarsu ce a ke cewa suyi wasu abubuwa.
Lura da irin wadannan matsalolin ne ya sa wasu kungiyoyi suka dage wurin fadakarwa. Amina Kadir shugabar 'yan jarida masu kare hakkin bil'Adama ta fannin kiwon lafiya tace ya taimaka sosai wajen kawo fahimta.
Shekaru goma sha biyar ke nan da ake kebe wannan rana domin mata masu aikin karbar haihuwa saboda haka ne suka kira mata su kai zuciya nesa.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Facebook Forum