Wadanda suka baro kasashensu saboda wasu dailai da dama kamar talauci da fatara da yunwa da yake-yake da rikicin siyasa ko na addini zasu samu taimako daga hukumar.
Malam Hamza Mustapha wakilin Majalisar Dinkin Duniya, MDD, mai kula da 'yan gudun hijira dake Agades, yace kowa ya san Agades gari ne da mutane suke ratsawa ta cikinsa domin su wuce zuwa Turai ko kuma su nemi sabuwar rayuwar da ta fi wadda suka bari a kasashensu.
A cewarsa a cikin mutanen dake gudun hijira akwai wasu ba kudi ba ne ya damesu. Suna gudu ne domin su tsira da rayukansu ko kuma 'yancinsu. Irin wadannan mutane basa tunanen komawa gida domin walau su rasa rayukansu ko kuma a jefasu gidan kaso idan sun koma.
A shekarar 2016 an kiyasta 'yan gudun hijira sama da 300,000 a Jamhuriyar Niger, acewar darakta mai kula da 'yan gudun hijiran cikin gida, Madam Abdulkarim Fodi, wadansu ceton rai ne ke sa basu iya komawa kasashensu. Ta bada misali da mutanen kasar Mali dake tserewa suna shiga kasar Nijar.
'Yanzu 'yan gudun hijira 166,000 ne 'yan kasashen Najeriya da Mali ke zaune cikin sansanonin 'yan gudun hijira a jihohin Tilaberi, Diffa da Yamai
Ofishin na Agades zai dinga bada bayanai ga masu neman mafaka.
Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani.
Facebook Forum