Tun da sanyin safiyar Alhamis din nan ne kotun ta zauna a cikin wasu tsauraran matakan tsaro a Dutse, babban birnin jihar Jigawa.
Ranar Talata lauyoyin dake kare Sule Lamido suka mika takardun neman belinsa bayan ya musanta tuhumar da gwamnatin jihar Jigawa keyi masa cewa yana yunkurin tunzura 'yan Jigawar game da zaben kananan hukumomin jihar dake tafe.
Alkalin ya karanto hujjojin da lauyoyin Sule Lamido suka bayar na neman belinsa. Lauyoyin sun ce yana da 'yancin a bada belinsa kamar yadda kundun tsarin mulkin Najeriya yayi tanadi.
Duk da sukar da lauyoyin gwamnatin jihar suka yi alkalin kotun yace kotun ta gamsu da dalilan da lauyoyin Sule Lamido suka gabatar. Kotun ta bada belinsa ba tare da gindiya masa wasu sharudda ba.
Mai Shari'a Usman Lamido yace kotun tayi la'akari da cewa Sule Lamido mutum ne mai mutunci a idon jama'a kuma ya rike mukamai da dama a kasar tare da zama gwamnan jihar har na tsawon shekaru takwas.
Kotun ta dage sauraran karar zuwa ranar biyar ga watan Yuli idan Allah ya kai rai.
Barrister Yakubu Abdullahi Ruba daya daga cikin lauyoyin dake kare Sule Lamido yace alkali yayi anfani da basirar sa, da shari'a yayi abin da dace. Yace zasu yi duk abin da zasu yi, domin tabbatar da an yi watsi da karar a karshe.
Su kuma lauyoyin dake kare bangaren gwamnati sun ce an basu umurnin kada su ce uffan akan maganar ga manema labarai.
Facebook Forum