Rikicin na Boko Haram ya tagayyara nakasassu irin su guragu da makafi da kutare da kuma kurame, baicin wadanda suka rasa rayukansu.
Rikicin ya lakume rayuka da dama ,baya ga wasu dubban da aka tilastawa gudun hijira ,kuma wani fannin da ba’a cika maida hankali ba shine halin da nakasassu suka shiga.
A wajen wani taron masu ruwa da tsaki na sabuwar kungiyar nakasassun Najeriya ta Progressive Disabled Forum,PDF,Komred Ibrahim Alhassan Ganye, dake zama shugaban kungiyar a Najeriya yace rikicin Boko haram ya maida wasu nakasassu baya,kuma abun takaici kawo yanzu hukumomi da kuma kungiyoyin agaji basu tunawa dasu. Babu tallafin da ake badawa domin tada komadar al’ummomin da rikicin Boko Haram ya shafa.
A don haka ne ma shugaban kungiyar ya mika kukansu ga gwamnatocin arewa da kuma kungiyoyin bada agaji da su tuna dasu.
Ita kuwa Patience Briston dake cikin wadanda rikicin Boko Haram ya nakasa biyo bayan tashin wani bom da ya rutsa da ita a garin Maiduguri,tace an maida su saniyar ware.
Kafin dai wannan rikici na Boko Haram gwamnatocin jihohin kan taimaka wajen kafa cibiyoyin koyon sana’a ga nakasassu shirin da a baya kwalliya ke biyan kudin sabulu.
Kodayake kullum dai gwamnatocin jihohi kan ce suna nasu kokari ,to amma kuma sukan danganta rashin kudi da zama kanda –garkin halin da nakasassun ke ciki,kamar yadda gwamnan jihar Adamawa Sen.Muhammadu Bindow Umaru Jibrilla ke cewa.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.
Facebook Forum