Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Yace Donald Trump Yana Kara Nuna Rashin Cancantar Maye Gurbinsa


Shugaban Amurka Barack Obama.
Shugaban Amurka Barack Obama.

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya fada jiya Lahadi cewa, a takarar da a keyi ta maye gurbinsa dan takarar Republican Donald Trump ya na nuna rashin cancantarsa da wannan ofis a kullum.

Obama dai ya goyi bayan yar jam’iyyarsa ta Demokrat Hillary Clinton a ranar 8 ga watan Nuwamba sannan yayi magana akan goyon bayan nata a wajen wani taro da akayi a Las Vegas, dake jihar Nevada.

A kwanan nan Trump ya yawaita korafi akan an shirya masa magudi akan yadda zaben zai kasance, abinda Obama yace hakan yana nuna Trump yana faduwa ne.

Obama yace “Wannan yana nufin baka da karfin halin da ya kamata ka yi wannan aiki, saboda akwai lokuta da dama da abubuwa suke yin zafi . Akwai lokuta da dama da abubuwa basa yiwuwa yadda kake so dole kayi hakuri ka jira.”

Clinton ma ta bada sako makamancin haka yayin da take taron kamfe a garin Charlotte dake Jihar Carolina ta Arewa, tace duk da banbance banbancen ra’ayi dake tsakaninta da shuwagabannin kasa da kuma ‘yan takara bata taba tantamar ko baza su iya jagorancin wannan kasa ba.

Trump yaje Naples , Florida a jiya Lahadi inda ya jaddada maganar sa ta bin diddigin cin hanci da rashawa kuma ya baiyana damuwarsa a kan yadda Clinton ta karya dokar gwamnati. Clinton dai ta fuskanci tambabyoyi da yawa kwanankin nan akan amfani da email na na kashin kanta a lokacin da take Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka, abinda tace kuskurene.

XS
SM
MD
LG