Majalisar dinkin duniya zata tallafawa sansanonin ‘yan gudun hijira dake arewa maso gabashin Najeriya, da kimanin Naira miliyan dubu uku da dari bakwai, masamman a jihar Borno inda yara ke mutuwa.
Jami’in na majalisar Stephen Obirian, a sanarwar da hukumar ta fitar yace wannan hanya ce ta ceto ‘yan gudun hijirar da al’umar yankin maza da mata sun ji jiki domin illar ‘yan ta’adda.
Wannan yazo ne daidai lokacin da rahoto mai inganci ke nuna ‘yan gudun hijirar dake sansanonin gwamnati na mutuwa saboda rashin wadatar abinci, inda kusan kullum kimanin mutane talati akasari yara ke mutuwa.
Babban sakataren majalisar dinkin duniya Ban Ki Moon, yace dalilin karawa Najeriya kudi shine domin kawo sauye sauye masu ma’ana, halin ni ‘yasu da jama’a ke ciki a arewa maso gabas babban abin damuwane .
Ya kara da cewa majalisar zata ci gaba da hada kai da Sauran hukumomi na tallafi na duniya domin kaiwa yankin arewa maso gabashin Najeriya agaji gaggawa.
Shima babban hafsan rundunar Sojan kasan Najeriya Janar Tukur Yusuf Burutai, yace rundunar zata ci gaba da baiwa wadanda kalubalen tsaro ya shafa magani kyauta.