Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ficewa daga Tarayyar Turai Ya Sa Birtaniya Sake Tsunduma cikin Rudani


Firayim Ministan Birtaniya, David Cameron
Firayim Ministan Birtaniya, David Cameron

Burtaniya ta dada tsunduma cikin rudami jiya Litini, a daidai lokacin da su kuma jami'an kungiyar Tarayyar Turai ke ta kai komon nemar mafita, game da kuri'ar ficewa daga kungiyar da 'yan Burtaniya su ka kada.

'Yan kasar dai sun jefata cikin rudani abin da wasu ke cewa, shi ne rudu mafi muni ga kasar tun bayan yakin duniya na biyu.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka ya yada zango jiya Litini a birnin London, inda ya jaddada abin da ya kira dangantaka marar dusashewa tsakanin Amurka da Burtaniya.

Kerry ya bayar da tabbaci ga Burtaniya cewa dangantaka ta musamman tsakanin kasashen biyu ba za ta canza ba don ficewar Burtaniya daga Tarayyar Turai. Da ya ke magana bayan wani taro jiya Litini da Sakataren Harkokin Wajen Burtaniya Philip Hammond, babban jami'in diflomasiyyar na Amurka ya ce "ga alama yanzu ne ma dangantakar ta fi muhimmanci saboda tababar da ke tsakanin jama'a." Ya kara da cewa huldarsu za ta cigaba da zama, abin da ya kira, "kakkarfa kuma mai muhimmanci."

Jami'an gwamnatin Burtaniya sun kashe daukacin jiya Litini su na ta kokarin daidaita al'amuran da wannan kuri'ar da birkitar ta yadda kasuwannin hannu jari da takardar kudin Burtaniya ta 'pound' darajarsu ta fadi a rana ta biyu.

A jawabinsa ga Majalisar Dokokin Burtaniya tun bayan kada kuri'ar, Firaminista David Cameron ya ce tattalin arzikin Burtaniya na da karfin fuskantar wannan rudun. "A bayyane ta ke cewa kasuwanni sun rikice. Akwai kamfanonin da ke tunanin yadda za su yi da jarinsu, kuma dama mun san cewa al'amarin ba zai zo da sauki ba," a cewarsa.

XS
SM
MD
LG