Kimanin watanni uku da mutuwar karamin ministan kwadago, James Ocholi, 'yan kabilarsa daga jihar Kogi suna kai komo domin ganin shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya maye gurbinsa da wani daga kabilar Igala, kabilar shi James Ocholi.
Lura da halin duba cancanta da Shugaba Buhari ke yi wajen nada minista, ba karbar suna daga gwamnoni ba ya sa 'yan siyasar jihar suna rubuta takardu inda suke ambatar sunayen wadanda suke ganin sun cancanta, suna mika su fadar shugaban kasa.
Kabilar Igala, kabila mafi rinjaye a jihar Kogi, ta mika bukatar a dauko wanda zai maye gurbin James Ocholi daga yankinsu. Suna cewa rasuwar Abubakar Audu ya sa Yahaya Bello dan kabilar Ebira ya zama gwamna.
Alhaji Muhammad Sanusi dake kan gabar tawagar ya bayyana dalilan da yake gani suna da mahimmanci wajen rubuta wasikar ga Muhammad Buhari. Yace yanzu a jihar Kogi gwamna ya fito ne daga kabilar Ebira. Kakakin majalisar shi ma Ebira ne. Alkalin alkalan jihar Ebira ne.Jakadan da aka zaba kwana kwanan nan shi ma Ebira ne. Yana fatan shugaban kasa zai tuna da su Igala da yawansu ya kai kashi 58 na duk jama'ar jihar. Yace suna fata idan zai nada minista daga jihar ya dauko daga kabilarsu.
Akan tsarin mulkin kasar Umar Zaga yace korafinsu al'amari ne na mulkin dimokradiya. Idan shugaba ya ga suna da gaskiya yana iya saurara masu amma ba dole ba ne a hukumance, sai ya nada minista daga wata kabila ba. Abin da doka tace shi ne ya dauko daga jiha.
Ga karin bayani.