Jami’an ‘yan sandan dake binciken kisan gillar da aka yi wa wata ‘yar majalisar dokokin ta Ingila, sun ki tabbatar da cewa kisan nata na da wata alaka da akidojin masu ra’ayin ‘yan mazan jiya na Biritaniyar.
Mutane dayawa da suka ganewa idon afkuwar harin da Thomas Mair mai shekaru 52 da haihuwa ya kai kan ‘yar majalisar, sunce kafin harin an ji shi yana ihun cewa “Birtaniya ce ta farko” sannan ya harbe ta har sau uku, kuma ya caka mata wuka ya kuma rike gashinta ya jata yayin da take zubar da jinni.
Kungiyar da ke amfani da kalmar ‘Birtaniya ce ta farko’ wadda ke kamfen din Birtaniya ta fice daga kungiyar tarayyar Turai, tace bata da hannu cikin wannan harin, haka kuma shugabannin kungiyar sun yi Allah wadai da harin.
Sai dai ‘yan sanda na kokarin gano dalilin da ya haddasa wannan aika aika.
Masu binciken dai sun binciki gidan Mair’s domin neman shedar dalilin da yasa ya aikata kisan. Wata kungiyar dake Amurka dake kula da kungiyoyi masu ra’ayin mazan jiya, sunce maharin ya dade yana goyon bayan wata kungiyar yan Nazi.