Kungiyar ‘yan bindiga na Niger Delta Avengers, na neman gurgunta tattalin arzikin Najeriya, masamman a ‘yan kwanakin nan bisa la’akari da mummunar hare hare da kungiyar ke kaiwa kamfanonin aiyukan hakar mai a yankin Niger Delta, harin baya bayan nan dai shine wanda kungiyar tayi ikirarin kawai kan kamfanin Chevron, mallakar kasar Amurka.
Kungiyar dai ta sanar cewa tayi watsi da duk wani shiri na sulhu da gwamnatin Najeriya, domin kawo karshen hare hare da take kaiwa,a baya dai an ruwaito cewa Ministan albarkatun man kasaIbe Kachikwu, yana cewa gwamnati zata soma da ‘yan sabon kungiyar na Niger Delta Avengers.
Kungiyar dai tace zata fito da wasu sabbin dabaru domin fadada hare haren ta na zamani akan kamfanonin aiyukan hakar mai a yankin na Niger Delta, kuma shirinta na nan na soma kakkabo jirage da suka ratsa ta yankin ta na Niger Delta Mai arzikin mai ta kuma kira kafanoni aiyukan hakar mai da cewa masu kunnen kashi ne.
Wasu daga cikin mazauna yakin na Niger Delta kamar Mr. Ehirus, cewa yayi gwamnatin da ta gabata ta fito da samar da aiyukan yi ga ‘yan bindigan yakin Niger Delta da kuma tura su kasashen waje domin yin karatu, sai dai kuma a wannan karo ba’a fido da wannan shirin ba wanna yana cikin abinda ya kara dagula lamarin, amma dai idan za’a bi hanya ta sulhu domin samun zaman lafiya a yakin toh muna bukatar hakan.
Ita kuwa Mrs Ari, cewa tayi janye Sojojin da aka yi bai da amfani domin hakan zai kara sa tsaro ya tabarbare babu wani dalilin janye Sojojin domin kasancewar Sojoji a wuri yana hana abubuwa da dama, domin mu dai zaman afiya muke so.
Hare haren da Niger Delta Avengers ke kaiwa akan butatayen mai da iskar gas yas dimbin man da kasar ke hakowa a kullum yayi raguwar da bai taba yin irinta ba akusa shekaru ashirin.