Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka da India Zasu Dauki Matakan Rage Makaman Kare Dangi


Firayim Ministan India Modi da Shugaban Amurka Barack Obama
Firayim Ministan India Modi da Shugaban Amurka Barack Obama

Shugaban Amurka Barack Obama, da Firayim Ministan India Narendra Modi, sun sake nuna irin dangantaka mai karfi dake akwai tsakanin kasashensu biyu.

Kasashen su ne suka dara sauran a yawan jama'a bisa tafarkin demokuradiyya. Shugabannin biyu sun gana ne jiya Talata a fadar White House ta shugaban Amurka.

A hira da Muryar Amurka, wani masani wanda yake aiki da wata cibiya dake nan birnin Washongton DC, yace akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin shugabannin biyu.

Shugabannin biyu suka ce sun dukufa wajen sanya hannu kan yarjejeniyar da aka kulla kan sakewar yanayi a Paris, nan da karshen shekara, kodashike basu ayyana lokaci ba, kamar yadda wasu suka sanya tsammani. Shugaba Obama ya godewa Firayim Minista Modi saboda dagewarsa na amfani da tsabtataccen makamashi.Tareda Modi a gefen hannun damarsa a ofishinsa, bayan da suka kammala zagaye na farko na shawarwari, Mr.Obama yace, "Jigo garemu duka biyu shine yadda zamu habaka ko bunkasa tattalin arziki, da kuma kawarda talauci tsakanin al'umarsu....".

A nasa bangare Firayim Minista Modi,ya nuna cewa irin yawan matasa miliyan 800 kasa da shekaru 35 da India take da su, wadanda idan kasashen biyu suka yi aiki tare, basisarsu zata taimakawa al'umma.

Haka nan shugabannin biyu sun yi shawarwari kan batutuwan tsaro,da kuma karfafa matakan hana yaduwar makaman kare dangi.

Shugaban Amurka da Firayim Ministan India
Shugaban Amurka da Firayim Ministan India

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG