To saidai gwamnatin jihar tace duk wanda ya koka dangane da rashin samun albashi akwai dalili.
Kimanin watanni hudu ke nan wasu ma'aikata da yawansu ya dara dubu daya basu samu ko sisin kwabo ba daga cikin albashinsu. A cikin ma'aikatan har da wadanda suka je kasashen waje domin karo karatu bisa amincewar gwamnatin jihar.
Wasu dake karatu a kasar Malaysia sun shaidawa Muryar Amurka cewa bayan an tantancesu an biyasu albashin watan Fabrairu sai kuma aka tsaya nan ba tare da basu wani dalili ba.. Sun ce sun mika takardun da gwamnati ta bukata amma har yanzu shiru kamar an shuka dusa.
Kungiyar kwadago ta jihar tace tana sane da matsalar kuma tana kokarin shawo kanta. Kwamred Yahaya Idris Ndako shugaban kungiyar kwadago reshen jihar yace sun gayawa kamfanin dake tantance ma'aikata cewa wadanda suke karatu a waje sun je da yaddar gwamnati ne. Wajibi ne a biyasu albashinsu, sun kuma rubutawa gwamnati ta biyasu.
To saidai ita gwamnatin tace a yanzu tana tantance ma'aikatanta saboda haka duk wanda ya koka dangane da rashin samun albashi to akwai alamar tambaya kamar yadda kwamishanan kudin jihar Alhaji.Ibrahim Balarabe ya fada.
Yace duk wanda ma'aikatarsa ta shaida ya je karatu babu yadda za'a dakatar da albashinsa. Saidai idan ma'aikatar bata sa sunan mutum ba to wannan ba laifin gwamnati ba ne. Alhaji Balarabe yace a tantancewar da suke yi sun bankado wasu da suke karbar albashi biyu, wasu kuma suna karban albashin da ba nasu ba ne.
Ga karin bayani.