A jiya Litinin ne aka gudanarda tarukan zanga-zanga a birane akalla guda uku na kasar Kenya, inda kafofin watsa labarai suka ce ‘yansanda sun bindige akalla mutum guda a yammacin kasar.
A can babban birnin Kenya, Nairobi, ‘yansanda sun zagaye hedikwatar hukumar zaben kasar, inda suka kwashe yini guda domin tsoratar da masu zanga zangar da suka mayar da ita wurin zanga zangarsu na wajen mako guda.
Masu zanga zangar dai basu samu damar isa harabar hukumar ba, saboda ‘yansanda sun harba barkonan tsohuwa da watsa ruwan zafi wajen tarwatsa mutane kusan 100, kafin su sami damar kusantar harabar hukumar.
Kafin wannan ma ‘yansanda sun harbawa wasu kananan kungiyoyin masu zanga zanga barkonan tsohuwa a jiyan, ciki harda wata kungiya daga garin Kibera, da mutane masu yawa daga Nairobi.
Masu zanga zangar dai sun sami kutsawa ofishin hukumar zaben mai zaman kanta da haraba hukumar, a biranen da suka hada da Mombasa da Kakamega da Kisumu. Wakilin gidan jaridar Standard Newspaper, Phillip Orwa, ya fadawa wannan gidan radiyon cewa, mutum daya ya rasa ransa wasu hudu kuma sun raunata.