Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Ta Bukaci Amurka Ta Kawo Karshen Sintirin A Gabarta,


Kasar China ta bukaci Amurka ta kawo karshen sintirin da ta ke yi daura da gabarta, bayan wani abin da Hedikwatar Tsaron Amurka ta Pentagon ta kira, "gamo mai hadari," tsakanin wasu jiragen yakin China sanfurin jet da wani jirgin yakin Amurka.

Pentagon ta ce wasu jiragen yakin China samfurin jets sun tasa keyar wani jirgin saman Amurka na sintiri, yayin da ya ke shawagi irin na yau da kullum ranar Talata, a sararin saman kasa da kasa a yankin Tekun Kudancin China.

To amma mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen China Hong Lei, ya fadi yau Alhamis cewa abin da Pentagon ta ce game da al'amarin ba gaskiya ba ne.

"Wasu jiragen yakin China samfurin jet su biyu ne su ka gano tare da sa ido kan wani jirgin Amurka kamar yadda doka da ka'ida su ka tanada." Ya kara da cewa, "Jiragen yaki samfurin jet din sun cigaba da barin tazara marar hadarin tsakaninsu da jirgin na Amurka, kuma sam ba su dau wani mataki mai kasada ba."

XS
SM
MD
LG