An sami rahoton bacewar akalla iyalai dari biyu a Sri Lanka kuma ana fargabar ta yiwa laka ta binnesu biyo bayan ruwa kama da bakin kwarya da aka yi, a cewar kungiyar bada agaji ta Red Cross ta Sri Lanka yau Laraba.
A wata sanarwa da kungiyar ta Red Cross ta fidda yau ta yanar gizo, ta ce an tura ma’aikatan jinkai tun da safe tare da jami’an gwamnati wajen kuma ta ce sun iya ceto mutane 180, duk da daukewar wutar lantarki da aka samu a kauyukan da dama dake gundumar Kegalle.
Kungiyar agajin ta Red Cross ta kuma ce ya zuwa yanzu an gano gawarwakin mutane 13.
Ruwan da aka yi ya haddasa ambaliyar ruwa a wasu birane ciki har da Colombo. An kuma rufe makarantu a fadin kasar yau Laraba saboda rashin yanayi mai kyau.
Cibiyar Sarrafa Masifu ta Sri Lanka ta bada rahoton mutuwar mutane 11 suka mutu ta hanyar wutar lantarki da kuma zaftarewar kasa cikin ‘yan kwanakin da suka gabata.