Majalaisar dattijan Amurka ta amince da kasafin kudi dala miliyan dubu daya da miliyan dari domin a yaki cutar Zika, kasa da abunda gwamnatin shugaba Obama ta nema, amma kuma ya ninka abunda majalisar wakilai ta kasafta.
Jiya Talata, majalisar da jam'iyyar Republican take da rinjaye ta amince da kasafin da kuri'u 68-29 bayan da majalisar tunda farko taki ta amince da duka abun da gwamnatin ta nema,wace ta gabatar cikin watan Febrairu, sakamkon gargadin da kwararu ta fuskar kiwon lafiya suka yi cewa cutar tana iya bazuwa a sassan Amurka mai yawa.
Cutar da sauro ke yadawa tana iya haddasa mummunar nakasa ga jarirai, wacce aka danganta da matsaloli da suka jibanci kwakwalwa.