Taron ya zo ne a daidai lokacin da tattalin arzikin kasar ya komade saboda faduwar farashen man fetur a kasuwannni duniya lamarin da ya tilasta wasu jihohi dogara da gwamnatin tarayya kacokan.
A wurin taron Shugaba Muhammad Buhari ya bada tabbacin cewa gwamnatinsa a shirye take ta ba kowace jiha hadin kai domin daukan matakan da suka kamata jihar ta dauka domin dogara da kanta.
Muhammad Buhari ya kara nanata matsayin gwamnatinsa ta tabbatar kowace jiha ta dauki matakan da zasu kaiga hako dukan ma'adanan da take dashi da kuma bunkasa sha'anin noma domin jihohin Najeriya su iya ciyar da kansu har ma su fitar da albarkatun noma waje.
Dr Mustapha Inuwa shugaban shirya taron na jihar Katsina yace gwamnan jihar ashirye yake ya tabbatar an aiwatar da duk abubuwan da aka shirya za'a yi. Yace aiwatar da ayyukan ya zama masu dole saboda kason kudin da suke samu daga gwamnatin tarayya yana raguwa kowane wata. A yanzu kusan kananan hukumomi 28 na jihar basa iya biyan albashi sai gwamnati ta cika masu. Saboda haka ya zama dole a tashi tsaye a nemi kudaden shiga.
A wani bangaren kuma Alhaji Mustapha Ado shugaban kamfanin Amasco Oil ya yi tsokaci akan alfanun taron da 'yan kasuwa suka halarta. Yace wadanda suke sayen man fetur ba dadin yin hakan su keyi ba saboda haka komawa kan ma'adanai da noma, shugabannin Najeriya sun yiwa kansu gata ne. Al'umman Najeriya kuma zata kubuta daga dogaro ga mai kawai.
Ga karin bayani.