Yayinda yake jawabi a wurin taron, ministan harkokin cikin gidan Najeriya Janar Abdulrahaman Dambazau mai ritaya, yace gwamnatin tana kokari ne ta ga ta cika alkawuran da ta yiwa al'umma lokacin zabe.
Janar Dambazau yace fa'idar taron nada yawa. Na daya an yiwa mutane alkawari kuma akan alkawarin suka jefawa gwamnati kuri'unsu. Na biyu Shugaban kasa Muhammad Buhari mutum ne mai cika alkawari. Dalili ke nan ya ga yakamata a yiwa mutane jawabi, su fadawa mutane abubuwan da gwamnati ke yi. Ban da haka a kuma ba jama'a damar su yi nasu tambayoyin. Hakinsu ne su yi tambayoyin domin su ne suka zabi gwamnatin.
Janar Dambazau ya cigaba da cewa idan gwamnati na kan hanya jama'a su fada masu. Idan kuma sun kauce hanya a fada masu.
Gwamnati ta fito da abubuwa guda uku. Na farkon shi ne harkar tsaro. Abu na biyu batun farfado da tattalin arzikin kasa. Abu na uku shi ne yaki da cin hanci da rashawa.
Dangane da cewa dubban mutane suke neman shiga aikin 'yansanda saboda dubu goman da za'a dauka, Janar Dambazau yace babu mamaki saboda mutane da dama basu da aikin yi. Yace amma za'a tantancesu da yin adalci a dauki wadanda suka dace.
Ga karin bayani.