Kungiyar Taliba ta Afghanistan ta tabbatar da cewa ta tura manyan wakilanta zuwa Islamabad don tattaunawa da jami’an Pakistan, tana mai cewa tana sa ran za'a sami maslaha a ganawar don ci gaba kasashen biyu.
Wani mai magana da yawun kungiyar ‘yan bindigar ya fadawa muryar Amurka yau Laraba cewa wakilan kungiyar ta Taliban su tashi ne daga ofishinsa da ke Qatar don tattaunawaa game da dangantakar kut-da-kut, kasuwanci tsakanin kasashen biyu.
Sai dai jami’an Pakistan ba su ce uffan ba akan kasancewar ko dalilin zuwa wakilan Taliban din.
Bayanai kafofin diflomasiyya sun tabbatarwa muryar Amurka cewa wakilan Taliban suna so a yi ganawa da wakilan Pakistan, wanna wani yunkurin ne da Islamabad ta ke yi na yin ganawar samar da zaman lafiya tsakanin gwamanatin Afghanistan da Taliban.