Jami’in na hukumar raya kasashe ta Amurka wato USAID mai suna Xulhaz Mannan, ya taba aiki da ofishin jakadancin Amurka da ke Dhaka, a matsayin mai kula da harkokin baki.
Wasu mutane biyar ne suka far wa Xulhaz da abokin nasa dan shekaru 26 Tanay Mojumdar wanda shima mai fafutukar kare ‘yan luwadin ne. Mutanen sun yi badda kamanni ne da yin shigar masu kai sakonni, inda suna shiga suka daddatsa su.
Mannan dan shekaru 35, shine editan wata Mujalla daya tilo a kasar mai suna Roopban da ake bugata game da fafutukar kare ‘yan luwadi da makamantansu. Har yanzu ‘yansanda ba su gano wadanda suka kashesu ba.
Amma kwamishinan ‘yansandan birnin Dhaka Asaduzzaman Mia yace, wannan kisa ne da aka shirya. Wato an dade ana hararsu. Yana kuma sa ran zasu kama wadanda suka aikata kisan bisa wasu shaidun da suka lura da su a inda aka yi kisan.
An yiwa wani dansanda da mai gadi rauni a lokacin da suke kokarin kama maharan, sannan shaidu da dama sun ce wadanda suka yi kisan sun ta kabbara Allhu Akbar, a lokacin da suka kashe su suna barin wajen.