Dawowar majalisar ke da wuya daga hutun makonni biyu sai takadda ta kunno kai akan kasafin kudin bana da majalisar tace lallai shugaban kasa ya rabtaba hannu ba tare da bata wani lokaci ba.
Kacenacen ya kunno kai ne bayan da majalisar ta kammala aikinta akan kasafin kudin ta mikawa gwamnati. A lokacin ne gwamnati ta yi zargin an cire nera biliyan 60 da ta ware domin gina layin dogo daga Legas zuwa Calabar.
Shugaban kula da kasafin kudi a majalisar wakilai Abdulmunmuni Jibrin yace babu gina layin dogo daga Legas zuwa Calabar a kasafin kudin. Ya sake nanatawa babu wani abu kamar gina layin dogo daga Legas zuwa Calabar. Abun dake cikin kasafin shi ne layin dogo daga Legas zuwa Kano.
Alhaji Jibrin ya cigaba da cewa a cikin aikin da kwamitin kasafin kudin majalisar ya yi sun fahimta cewa an karawa yankin sufuri wajen biyan 54 domin kudin da aka sa kan layin dogo daga Legas zuwa Kano ba zai isa ba saboda haka suka kara biliyan 39. Cikin sauran kudin suka sa a gyara filayen jirgin sama dake Legas, Kano, Enugu da dai sauransu.
Abdulmunmuni Jibrin yace abun da ya bata masa rai shi ne zargin da ake yi cewa shi ya kwashi ayyuka ya kai Kano ko kuma Kiru da Bebeji. Ya nemi a yi masa adalci..
Shugaban kwamitin tsare-tsaren manufofin kudi na majalisar Timothy Ngolu Simon ya bada shawarar yadda za'a magance takaddamar. Yace idan shugaban kasa na son gina layin dogon daga Legas zuwa Calabar sai ya kawo sabon karin kasafin wa majalisa. Ba zata hanashi ba. Zata amince da karin. Bugu da kari shugaban nada 'yanci ya cigaba da yin anfani da kasafin har zuwa kashi hamsin cikin dari kafin a yi gyaran da yake so. Saboda haka shi bai ga dalilin da za'a hakikance akan sai an sake gyara kasafin gaba daya kafin a soma aiki dashi ba. Yana da ikon ya fara yin aikin da zai taimakawa jama'a.
Mr. Simon ya kira masu aiki da shugaban kasa su taimaka masa saboda abubuwa sun yi masa yawa. Dole ne su dinga gaya mashi gaskiyar dake zuciyarsu. Batun kasafin kudi ya wuce siyasa, abu ne akan yadda za'a cigaba da kasar.
Majalisar dattawa ta kira bangaren gwamnati ta hanzarta tabbatar da kasafin kudin ba tare da bata lokaci ba.
Ga karin bayani.