Malamai a kasar Liberia sunyi fatali da wani shirin kwaskwarima da gwamnatin kasar ke kokarin yiwa fannin ilmin kasar.
Malaman sunyi barazanar fadawa cikin yajin aiki, muddin gwamnatinn kasar tayi wannan gyaran da tayi aniyar yi wanda zai hada makarantun gwamnati da na masu zaman kansu.
Babban sakataren kungiyar malamai na kasar yace malaman sun ajiye ranar talata a matsayin ranar da zasu fara yajin aikin muddin akayi kunnen kashi da wannan bukata tasu.
Sai kuma yanzu haka gwambnatin kasar ta riga ta kulla yarjejeniya da wata makaranta da ake kira BRIDGE INTERNATIONAL ACADEMIA mai zaman kanta, wadda take anfani da tsarin fasahar zamani domin bunkasa ilmi ga kasashe masu tasowa.
Ministan ilmi na kasar George Werner ya shaidawa muryar Amurka cewa ba wai gwamnati na kokarin mayar da makarantun gwamnati na kudi bane, sai dai hada hannu da makarantu masu zaman kansu diomin bunkasa ilmi a kasar.
Ministan ya koka akan yadda ilmi ke tabarbarewa a kasar abinda yace hakan na bukatar mataki na musammam.