Yawan haduran motoci akan hanyoyin Najeriya na jawo damuwa a zukatan mutane dake zirga-zirga akan tituna musamman a yankuna da suka yi kamarin suna wajen samun hadari.
Wurare irinsu kwanar Langalanga a jihar Nasarawa, hawan kibo a jihar Filato ko kwanar mai saje kan hanyar Adamawa da wasu ramuka kan hanyar Abuja, Kaduna zuwa Kano ana yawan samun hadari. Akwai wata hanya kuma da ta fi ramuka daga Kontagora zuwa Minna a jihar Neja.
A Najeriya da wuya a yi tafiyar kilomita goma ba'a ga baraguzan wata mota ko motoci da suka yi hadari ba.
Mutuwar karamin minista James Ocholi daga Kaduna zuwa Abuja ta tayar da maganar rashin sahihancin tuki ga wasu direbobin.
Dan Majalisa Kazaure yace ya dace a samu dokar mallakar lasisin tuki mai inganci. Yace yanzu mace zata je banki a bude mata asusu amma sai ta bada kudi a je a yi mata lasisi kuma bata taba tuka mota ba. Yace yana shirin gabatar da wani kuduri akan lasisin tukin mota da zai tabbatar duk wanda ya mallaki lasisi ya iya tukin mota ne kafin ya samu.
Wani dan garin Potiskum dake jihar Yobe ya nuna takaicin yadda manyan motoci sukan mike hanyar Potiskum zuwa Maiduguri da hakan ya mayar da hanyar kunya-kunya. Yace babu ranar da za'a bi hanyar ba'a yi hadari ba tare da hasarar rayuka.
Ga karin bayani