Shugaban darikar Anglican a shiyar arewa maso gabas Bishop Benjamin Kwashi ya yiwa Muryar Amurka karin haske kan bikin na Easter.
Bishop Kwashi yace almajiran Almasihu ba zasu taba mancewa da tashinsa ba da abubuwan da ya yi da ma'anar abun da ya yi sabili da wasu dalilai:
Na daya tashinsa daga matattu ya nuna nasara da Allah ya yiwa Almasihu bisa kan mutuwa.
Na biyu tashinsa daga matattu ya nuna nasarar da Almasihu ya yi kan zunuban 'yan Adam. Wato shi ne ya sadakar da kansa domin shafe zunuban dan Adam gaba daya.
Na uku tashinsa ya nuna nasara bisa kan Shaidan.
Bishop Kwashi ya cigaba da cewa duk wanda ya san ma'anar dalilan guda uku da mahimmancinsu ga bil Adam Easter nada babbar mahimmanci ga mai bangaskiya.
Shi ma sakataren Tarayyar Eklisiyoyi a Najeriya ko TEKAN Rebaran Moses Ebuga yace Easter lokaci ne da al'ummar kirista zasu nuna kauna ga duk mutane. Yesu Almasihu mai kauna ne saboda haka yakamata kiristoci su zama masu kauna. Yadda Almasihu ya kasance mai jinkai haka kiristoci yakamata su kasance.
A halin da ake ciki rundunar tsaro a jihar Filato ta dauki kwararan matakan tabbatar da gudanar da bukukuwan lafiya. Kakakin rundunar tsaron Keften Ikedishi Iweha ya roki jama'a su bada rahoton duk wani take taken ta'adanci da suka hango.
Ga karin bayani
.