Shugaban Amurka Barrack Obama yau ya sauka Argentina domin ziyarar aiki na kwanaki biyu, wadda wannan ziyarar wata alamar jan kunne ne ga kasar da tattalin arzikin ta ya shiga cikin wani mawuyacin hali.
Haka kuma ziyarar tazo dai-dai da bikin cika shekaru 40 juyin mulkin da kasar Amurka ta mara wa baya.
Jirgin shugaba Obama ya sauka kasar da tsakar daren laraba amma fa lokacin kasar.Ya dai yada zango ne bayan tasowar sa daga ziyarar da yakai kasar Cuba.
Cikin tawagar tasa dai akwai Uwargida Michell tare da ‘ya’yan su, sai kuma surukar sa.
A wannan ziyarar dai shugaba Obama zai gana da shugaban kasar na Argentina Mauicio Macri wanda ya nuna alamun cewa yana son kyaskyawar huldan cinikayya da kasar ta Amurka dama wasu kasuwannin daban-daban.
A yau din ne dai ake sa ran shugabannin biyu suyi jawabi a wajen wani liyafar cin abinci.
Wannan ziyarar ta shugaba Obama yazo dai-dai da shekaru 40, lokacin da aka kawo karshen wani juyin kama karya wanda yayi dalilin mutuwa ko kuma bacewar mutanen da yawan su yakai dubu 30.
A gobe alhamis shugaba Obama zai ziyarci inda aka gina domin tuna wadanda suka mutu a wannan lokacin.