Inda gwamnoni da ministoci da kwararru akan sha’anin tattalin arziki a Najeriya, ke yin bita domin tsara hanyoyin da za a bi kasar wajen rage dogaro da ga albarkatun Man fetur, da komawa ga albarkatun Noma da kuma hakko ma’adanai.
A yanzu dai an himmatu ne akan tsarin samar da wutar lantarki, saboda taron ya fahimci cewa babu wani ci gaba da za a iya samu ta kowanne irin fuska a kasar ba tare da anyi nazari akan wutar lantarki ba.
Kamar yadda gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu, ke bayyanawa wakilin Muryar Amurka, Umar Faruk Musa, a gurin taron cewa maganar Noma itace babban gadon da Najeriya za tayi amfani da shi da dogaro domin samar da kudaden kasar waje zuwa cikin Najeriya. har ma yace manoman jihar Kebbi a shirye suke domin su samar da abincin da zai ciyar da Najeriya harma a fitar da shi kasashen ketare.
Wakilin Muryar Amurka, ya tambayi kwararre akan sha’anin tattalin arziki kuma tsohon minista na kudi, Dakta Mansur Muktar, cewa ta yaya za a yi dowawa akan abubuwan da suka shafi noma da hakko ma’adanai zai inganta tattalin arzikin Najeriya cikin dan karamin lokaci?
Dakta Mansur, ya amsa da cewa “bisa bayanai da akayi a taro ciki akwai abubuwan da za a iya yi wadanda suke cikin gaggawa za a samu nasara. Inda kuma ake ganin sai an ci gaba da nazari shine harkar wutar lantarki.”
Domin karin bayani saurari rahotan Umar Faruk Musa.