Rahotanni sun ce bala'in har ila yau ya jikkata wasu da dama a safiyar yau.
Girgizar kasar ta faru ne a arewa maso yammacin kasar da ke da tazarar kilomita 80 daga babban birnin kasar Kalamandu.
Lamarin ya zubar da gine-gine da katangun jama’a wanda hakan ya koro jama’a kan tituna a firgice.
Ragowar girgizar kasar mai karfin maki 6.6 ta sake aukuwa sa’a guda bayan na farko inda ya haifar da barnar da ta raunata mutane.
Yanzu haka dai masu aikin agaji na ci gaba da kai dauki ga wadanda abin ya rutsa da su.
Shima babban ginin nan na tarihi da aka gina tun a karnin 19 mai suna Ginin Kalamandu, ya zube inda ake zaton ya murkushe jama’a da dama.