Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Baltimore Ana Zanga-zangar Mutuwar Wani Baki a Hannun 'Yansanda


Wasu masu maci a Baltimore, Jihar Maryland Amurka
Wasu masu maci a Baltimore, Jihar Maryland Amurka

Mutuwar Gray a hannun 'yansandan Baltimore ta jawo zanga-zangar kin jinin 'yansanda

Daruruwan masu zanga zanga suna maci a kan titunan birnin Baltimore na jihar Maryland suna kira da a yiwa mutumin nan dan shekaru 23 da ya mutu a hannun ‘yan sanda farkon wannan makon adalci.

Kungiyar dake maci suna cewa, “ dare, da rana, muna neman a yiwa Freddie Gray adalci” Jiya Alhamis, sun tashi daga zauren taron birnin zuwa shelkwatar rundunar ‘yan sanda kafin su shiga layukan birnin. Ba a sami wani tashin hankali ba, sai dai ‘yan sandan birnin Baltimore sun fada a dandalinsu na twitter cewa, an kama a kalla mutane biyu sabili da neman tada zaune tsaye da kuma lalata kaddarori.

Gwamnan jihar Marylad, Larry Hogan, ya umarci rundunar ko ta dogarawan tsaron jihar su taimaka wajen kiyaye doka da oda yayinda ake ci gaba da zanga zangar.

Mutuwar Gray, mako guda bayan kama shi ta haddasa zanga zanga kowacce wayewar gari.

Wani lauyan iyalin ya shaidawa Muryar Amurka cewa, an jiwa Gray mummunan rauni a gadon bayansa bayan da ‘yan sanda suka kama shi ranar 12 ga watan Aprilu.

Har yanzu ba a tantance musabbabin raunin da ya ji a gadon bayan shi ba, yayinda hukumomin jiha da na tarayya suke kan gudanar da bincike.

A ranar Lahadin da abin ya faru dai, Gray ya hada ido da wani dan sanda ne sai ya arce da gudu lamarin da ya sa ‘yansanda suka kama shi.Da suka bincikeshi sun samu wuka a kuibinsa, sai suka jashi zuwa cikin motarsu.

An ba ‘yan sanda shida hutun dole yayinda ake binciken musabbabin mutuwar mutumin.

XS
SM
MD
LG