Turawan zabe a Najeriya na ci gaba da bayyana sakamakon zabe a matakin kasa da jihohi da kuma mazabun ‘yan majalisar dokokin Kasar.
Yayin da ‘yan Najeriya suka zaku don jin sakamakon zabubukan da suka yi, wani abu da ke daukar hankali shine yadda ake samun soke sakamakon wasu runfuna abin da ke sa ba a iya ayyana dan takarar da ke da galaba amazabun.
Wakilan jam'iyyun hamaiya sun yi watsi da yadda a ke gabatar da sakamakon zaben shugaban Najeriya a wuni na biyu da fara gabatar da sakamakon.
Hukumar zaben Najeriya ta karbi sakamakon zaben shugaban kasa daga jihar Ekiti, wacce da ma ta kan zama ta farko a wajen tura sakamako.
A ci gaba da kidayar sakamakon zaben shugaban kasa na 2023 daga kananan hukumomin jihar Bauchi, zuwa yanzu Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ne ke kan gaba da rinjaye kan sauran abokan hamayyarsa.
A ranar Lahadi 26 ga watan Fabrairu 'yan daban suka kai hari a cibiyar tattara sakamakon zaben dauke da wukake da kuma sanduna amma jami'an tsaro suka fatattakesu, a cewar kamfanin dillancin labaran Reuters.
Jama’a masu zaman jiran sakamakon zaben da aka gudanar ne jiya Asabar 25 ga Fabrairun 2023.
Har yanzu hukumomin jihar ta Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ba su fayyace musabbabin gobarar ba, wacce ta lakume shaguna da dama.
Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta INEC ta ce zata gudanar da zabe ranar Lahadi 26 ga watan Fabrairu na shekarar 2023, a rumfunan zabe 141 a birnin Yenagoa da ke jihar Bayelsa sakamakon wani rikici da aka samu a wasu mazabu.
Masu zabe a sassa daban-daban na Abuja sun nuna gamsuwa kan aikin na’urar tanatnce masu kada kuri’a wato BVAS da hukumar zabe ke amfani da ita a babban zaben da bugin kirjin hanya ce ta magance magudin zabe.
An haifi Bola Ahmed Tinubu a ranar 29 ga watan Maris a shekarar 1952 a birnin Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya.
An haifi Mohammed Rabiu Musa da akafi sani da Rabiu Musa Kwankwaso shekaru 67 da suka shude a garin Kwankwaso na karamar hukumar Madobi da ke jihar Kano Najeriya.
Domin Kari