Shugaban Hukumar Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a cibiyar tattara sakamakon zabe da ke Abuja, inda ya ce an samu tsaiko a mazabu na hudu, shida, takwas, da sha hudu.
Farfesa Yakubu ya ce jami'an tsaro sun shawo kan lamarin, amma hukumar ta yanke shawarar dage zaben ne bayan da ma’aikatan wucin gadi na INEC suka bayyana fargabar komawa gudanar da zaben.
Shugaban na INEC ya kara da cewa hukumar zabe ta yanke shawarar gudanar da zaben a yau Lahadi, an cimma wannan shawarar ne bayan tattaunawa tsakanin jami’an hukumarsa da jami’an tsaro a jihar a cewarsa.
Yana mai cewa “Mun gana da hukumomin tsaro kuma mun yanke shawarar cewa za a kada kuri’a a rumfunan zabe 141 da kayan aikinsu suke a shirye tsaf, da safiyar Lahadi.
"Ku tuna ba zaben shugaban kasa kawai muke yi ba, har da na 'yan majalisar dokoki," abinda Yakubu ya fada wa manema labarai kenan.
Ya kara da cewa 'yan daba sun kai hari a rumfunan zabe dabam-daban kuma an sace akalla na’urorin BVAS guda takwas a sassan kasar.
Farfesa Yakubu ya bayyana cewa an samar da na’urorin BVAS da aka tanada don tabbatar da cewa ba a lalata aikin zaben kwata-kwata ba.