Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce sama da mutane milliyan casa’in da daya a Afirka suna rayuwa da cutar Hepatitis nau’in B ko C, wadanda suka kasance mafi hadarin cutar.
WHO ta ce akalla mutane miliyan dari biyu da sittin ne suke fama da cutar Asthma a fadin duniya.
A Kenya an samu raguwar masu kamuwa da cutar Maleriya da kashi 50 cikin dari a cikin shekaru goma da suka gabata kamar yadda ma’aikatar lafiya ta Kenya ta sanar da sabbin dabarun kawar da cutar zuwa 2030.
Mun jiyo ra’ayoyin wasu mazauna jihar Kano a Najeriya game da irin damuwar da suke da ita da maleriya, da kuma yadda suke kare kansu.
Ghana da Najeriya sun amince da sabon maganin rigakafin cutar maleriya da jami’ar Oxford ta kirkiro da shi. Maganin ya kawo kyakkyawan fata a yaki da cutar zazzabin cizon sauro.
Azumi yana haifar da bushewar ruwan jiki da kuma karancin yawu a baki a cewar masana, amma likitocin hakori sun bada wasu shawarwari.
Mujallar British Medical ta wallafa shawarwari yadda likitoci za su taimakawa marasa lafiya a cikin watan Ramadan.
Mabiya addinin Kiritanci sun kammala azumi da bikin hutun Easter, Musulmai a fadin duniya suna ci gaba da gudanar da azumin watan Ramadan, kamar yadda muka gani a Habasha.
Zaitun Mahmud Aminu, wani kwararre kan abinci mai gina jiki a Cibiyar nazarin abinci a Najeriya reshen jihar Kano, ya mana karin haske akan fa’idodin da suka shafi lafiya na azumi.
Minene tarin fuka kuma wadanne sababbin hanyoyi ne ake bi domin taimakawa wajen yaki da cutar ta tarin fuka. Mun samu karin haske daga Dr. Suraiya Muhammad Usman a Najeriya.
Kasashe a nahiyar Afirka suna ci gaba da kasancewa a fadake dangane da barkewar cutar Marburg. Tanzaniya ta ba da rahoton barkewar mummunar cutar na farko bayan an sami mutane 8 da alamun cutar 5 daga ciki sun mutu kuma yanzu haka ana sa ido kan wasu mutane 161 da ake hasashen sun yi mu’amala da su.
Yaran da har yanzu suke a kasar ukraine su na fama da lalurar damuwa sakamakon tashin hankali na yaki da suka gani.
Domin Kari