Dakta Hajar Mamman Nassir, Kwararriyar Likita a Abuja, Najeriya ta yi mana ƙarin bayani a game da yadda ake magance cututtukan da akai shakulatun bankagaro da su a cikin al’ummomi daban-daban.
Masana na ganin zogale da Malambe a matsayin kayan abinci masu gina jiki dake amfani musamman ga lafiya. Abubuwa masu gina jiki dake cikin nau’ukan abincin sun zarce na sauran nau’ukan abinci, lamarin dake bada gudummawa ga lafiya a cewar masana abinci.
Kwararriya kuma ‘yar kasuwa, Maryam Idris ta amsa tambayoyi wasu mahimman tambayoyi a game da fa'idodin zogale da kuma ire-iren abincin za su iya dakile kamuwa da cututtuka.
A Ghana gwamnati ta kirkiro da wata manhaja mai suna E-PHARMACY domin saukake hanyoyin siyan magungunan bature da kawarda masu sayar da magungunan marasa inganci dake illa ga kiwon lafiyan jama'a.Ana sa ran wannan manhaja za ta taimaka sosai muddin aka kara samun annoba kamar coronavirus a nan gaba.
Dr Shema Ahmad Abdulsadiq na sashin aikin zuciya a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, ya yi mana karin bayani akan mai ake nufi da matsalar bugun zuciya wato cardiac arrest a turance kuma ta yaya mutum zai iya shawo kan matsalar.
Menene ra'ayinku a game da shiga matsananciyar damuwa bayan haihuwa kuma me kuke ganin iyali ko al'umma za su iya yi don taimakawa macen da bayan ta haihu ta ji damuwa ko kuma ta shiga damuwa na makwanni?
Masana a fannin kiwon lafiya sun bayyana cewa wasu sabbin iyaye mata suna fuskantar damuwa bayan haihuwa ko PPD a turance, wanda ka iya zuwa da sauki ko kuma matsananciyar damuwa bayan sun haihu, lamarin da zai iya ɗaukar tsawon makonni ko watanni.
Dr Mahmoud Kawu Magashi na asibitin koyarwa na malam Aminu Kano, ya yi mana karin bayani akan matsalar bakin ciki ko matsananciyar damuwa bayan haihuwa.
Me kuke fatan ingantawa ko cimma a shekarar 2023? Ga wasu daga cikin ra’ayoyin ‘yan Najeriya akan wannan.
Dr. Fatima Anga, Likita a asibitin gwamnatin tarayya dake Jabi-Abuja ta yi mana bayani a kan abubuwan da ya kamata mutane su yi don kula da lafiyarsu a wannan sabuwar shekarar milladiya.
Ma'aikatar lafiya ta kasar Kenya ta ce ayyukan wayar da kai ta fasahar zamani kan ilimin saduwa da aka kaddamar don taimakawa wajen shawo kan matsalar daukan ciki a tsakanin ‘yan mata da basu manyanta ba a kasar ya samu matasa fiye da dubu 5 a yanzu.
Domin Kari