Kenya ta samu gagarumar ci gaba a yunkurin rage masu yawan kamuwa da cutar HIV cikin shekaru goman da suka gabata. An samu raguwar sabbin masu kamuwa da cuta da kaso 78% sannan an samu raguwar mutanen da AIDS yake sanadin mutuwar su da kaso 57%.
Farfesa Ibrahim Ummate, jami’in cibiyar jinyar koda ta asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri a Najeriya, ya yi karin bayani a game da matsalar cutar koda da kuma kalubalen maganinta.
A Zambia, hukumomi sun ce ana samun karuwar matasa mata masu kamuwa da sankarar mama a kasar. Haka kuma, ana samun karuwar wadanda ake gano cutar a tare da su bayan ta kai mataki mafi muni a kurarren lokaci.
Hukumar lafiya ta duniya ta kiyasta kiyasta cewa mutane miliyan 850 ne suke fama da cutar koda a fadin duniya, sannan cutar ta na sanadiyyar mutuwar sama da mutum miliyan 2 da dubu dari shida a kowace shekara.
Wannan na zuwa ne wattani 2 bayan da gwamnatin kasar ta janye matakin gaggawar lafiyar al’umma wanda aka ayyana tun shekarar 2022.
Wani kwararen likita a Najeriya, Dr Ibrahim ya yi karin haske a game da fida da mutum-mutumi.
A Afirka ta Kudu, an rungumi amfani da mutum-mutumi a aikin tiyata a zaman wani abin dogaro da shi nan gaba a fannin kiwon lafiya.
LAFIYARMU: Wani rahoto da kungiyar assasa ci gaba ta kasa da kasa, wato Global Action For Sustainable Development ta fitar a bana, ya ce kaso mai yawa na al’ummar Liberia na salwanta sakamakon ta’ammali da miyagun kwayoyi.
Shirin ya mafia hankalo kan kafewar jinin al’ada na mata wato menopause da kuma daukewar sha’awa da kwayoyin haihuwa a maza wato Andropause.
Shirin lafiyarmu na wannan makon, ya mai da hankali akan cututtukan Kansar da suka fi addabar mata a fadin duniya.
Hukumar Lafiya Ta Duniya ta sahalewa sabon maganin rigakafin zazzabin cizon sauro. Ana fatan za a gaggauta fitar da sabon maganin a kasashen Afirka a cikin watanni masu zuwa.
Dr. Hajara Asheikh Jarma, kwararriyar jami’ar lafiya a asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri, ta yi wa wakilyar mu Hussaina Muhammed karin bayani a game da masu fama da lalurar zabiya.
Domin Kari