Jihar Borno dake Najeriya ta shafe fiye da shekara goma ta na fama da matsalar tsaro. Hukumomin tsaro a jihar dai su na ci gaba da samun nasara a yaki da suke yi da masu aikata lafuka.
Ma'aikatar gandun daji ta Nijar ta bai wa wasu mazauna yankunan karkara horo domin sanin hanyoyin bi na samun tallafin gudanar da ayyukan dogaro da kai.
Rikicin Boko Haram ya mayar da dubban yara a arewa maso gabashin Najeriya marayu. Akasarin yaran su na fuskantar kalubale na rayuwa sosai. Amma wasu daga cikinsu, sun samu rayuwa mai kyau a jihar Sokoto.
Gwamnatin Amurka ta bai wa Nijar din gudunmowar jirgin sama samfarin Hercules C-130 domin taimakawa kasar a yakin da take yi da ‘yan ta’adda, da kuma kai daukin jin kai da ake bukata sakamakon matsalar tsaron.
A watannin baya, ‘yan bindiga a jihar Sokoto a Najeriya sun karbe iko a wasu garuruwa, inda har suke nada kansu a matsayin sarakuna, tare kuma da shata dokoki da tilastawa jama'a biyan haraji.
A ci gaba da fafutukar lalubo hanyoyin samun dawwamammen zaman lafiya a jihar Filato ta Najeriya, wata kungiya ta shirya wani taro na matasa a Jos, wanda ake fatan zai taimaka wajen kawo karshen tare hanyoyi da wasu ke yi da kai hare-hare kan matafiya.
Garin Bama a jihar Borno a Najeriya, ya na daga cikin wuraren da mayakan Boko Haram suka kori jama’a a shekarun baya. Shehun na Bama, Umar Ibn Shehu Kyari Ibn Umar Elkanemi ya ce su na gamsuwa da nasarorin da ake samu a halin yanzu.
Bayan wasu kwanaki da kai hari a wani gidan yari a jihar Filato, iyalin ma’aikacin gidan yarin da ya rasa ransa a lamarin, sun bukaci gwamnati da ta taimaka musu. Fiye da firsinoni 260 suka gudu a lokacin da aka balle gidan yari.
A baya bayan nan, gwamnan jihar Kano Ganduje ya yi ta kai ruwa rana da wasu jiga-jigan ‘yan jam’iyyarshi ta APC a jihar. Tsohon gwamnan jihar, Sanata Ibrahim Shekarau ya ce suna rikici da gwamnan mai ci ne saboda yadda aka mayar da su saniyar ware wajen gudanar da harkokin jam’iyyar a jihar.
‘Yan Najeriya da dama sun ce ba sa goyon bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin kasar ke shirin yi a shekara mai kamawa, inda suka ce ba sa son tukwicin Naira dubu biyar biyar a kowanne wata, domin rage radadin cire tallafin man.
A birnin Maiduguri dake arewa maso gabashin Najeriyar, kungiyar matan manyan jami’an sojin kasar ta rabawa ‘yan gudun hijirar rikicin Boko Haram kayan abinci, a wani yunkuri na kawar da yunwa a tsakanin su.
Maza na Fulanin Wodaabe sun gudanar da gasar nuna kyau ta jan hankalin ‘yan mata a Nijar.
Domin Kari