A ci gaba da bayyana wasu 'yan siyasar Amurka masu tasowa masu alaka kai tsaye da Afirka wadanda ke sauya fasalin siyasar Amurka da Muryar Amurka ke kawo muku, wannan ne labarin Oye Owolewa, wanda iyayensa suka fito daga Najeriya.
Tayoyin mota da aka jefar ka iya zama shara ko kuma kayan amfani. A Senegal, wasu dalibai sun kafa kamfani da ke sarrafa tsofaffin su zama abubuwan amfani.
Wasu masu aikin gyaran zoben azurfa da zinare a Kano sun nunawa Muryar Amurka yadda hanyoyin zamani ke tasiri sosai wajen bunkasa saa’arsu.
A wani yunkuri na inganta sha’anin kiwon lafiya a jihar Borno, kungiyar agaji ta Red Cross ta samar da motocin daukan marasa lafiya a wasu kananan hukumomin jihar, domin kai marasa lafiya asibiti idan bukatar hakan ta taso.
Kamar a sauran sassan Najeriyar daban-daban, jama’a na ci gaba da kokawa da tsadar gas na yin girki a birnin na Jos.
‘Yan bindiga a jihar Sokoto a Najeriya sun karbe iko a wasu garuruwa, inda har suke nada kan su a matsayin sarakuna, tare kuma da shata dokoki da tilastawa jama'a biyan haraji.
Wasan Zabuwa, wasa ne na shekara-shekara na Zabarmawa da Adarawa, ‘yan asalin Nijar dake zaune a kasar ta Ghana.
Tsohon shugaban kasar Nijar Mohamane Ousmane ya ce rashin shugabanci na gari na taimakawa wajen karuwar matsalar tsaro da kasar ke fama da ita.
Matan karkara a Kenya su na rungumar noman tsiron teku da ake kira seaweed a Turance da nufin yaki da talauci da kuma dogaro da kai.
Omar Fateh wanda iyayensu suka fito daga kasar Somaliya, dan majalisar dattijan Minneapolis Ta Kudu ne a Amurka, wanda yake cikin al’umomi daban-daban na kasashen waje dake sauya siyasar Amurka.
Sashin Hausa na Muryar Amurka ya shirya wani taro na tattauna matsalar tsaro da Nijar ke fuskanta. Masu sharhi kan al’amura a Nijar da dama ne suka halarci taron, wanda shugaban shashin Hausa na Muryar Amurka, Aliyu Mustapha Sokoto ya jagoranta.
Shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazoum a hira ta musanman da Muryar Amurka ya ce matsalar tsaro ce babban kalubalen da ya fuskanta tun da ya zama shugaban kasa watanni bakwai da suka wuce.
Domin Kari