Wasu masu bincike a Afirka, suna kirkirar fasahar amfani da murya wadda zata habbaka harsunan asali a Nahiyar.
A yankin Sahel na Afrika matsalar sauyin yanayi na kara munin rikice-rikice musanman tsakanin manoma da makiyaya.
Mazauna wasu sassa na birnin Maiduguri a jihar Borno a Arewacin Najeriya na ci gaba da kokawa da rashin wutar lantarki, tun bayan da mayakan Boko Haram suka lalata wasu turakun lantarkin.
An kammala wasan karshe na gasar kokawa ta gargajiya ta kasa karo na 42 a Jamhuriyyar Nijar inda ‘yan kokawa tamanin daga yankuna takwas na kasar suka fafata a wannan gasa mai farin jini.
Ga kadan daga cikin ra’ayoyinku game da tambayar da mu ka yi maku ta wannan makon a shafinmu na Facebook.
Yayin da wakoki na mawakan Afirka ke ci gaba da daukar hankali a duniya, da dama daga cikin masu fasahar waka a Najeriya na kallon wannan a matsayin wata dama ta yin suna da samun daukaka. Muryar Amurka ta zanta da DJ Cinch.
Yayin da shekara ta 2021 ta kare mun yin waiwaye kan matsalar satar mutane domin kudin fansa da kuma yadda al’ummomi ke daukan makamai domin kare kansu a Najeriya.
Mun waiwayi shekarar da ta kare ne inda muka samu zantawa da wani yaro dan shekara 15 wanda Allah ya horewa baiwar zane-zane. Yaron dai bai yi karatun boko ba, amma zanen da yake yi, tamkar wani babban mutun ne da ya yi karatu mai zurfi.
Mun kuma waiwayi baya a Nijar yadda huumomi a yankin Tillaberi na kasar suka dage dokar amfani da babura a 2021 bayan hani na shekara hudu.
Za mu fara shirin na wannan makon ne daga Najeriya, inda kiristoci, suka bi sahun kasashen duniya wajen shiryawa shagulgulan kirsimeti.
Yanzu kuma za mu leka shafinmu na Facebook don jin irin ra’ayoyin da ku masu kallo kuke ajiye mana game da tambayar da mu ka yi muku ta wannan makon.
To a Nijar ma, kiristoci sun yi shiri sosai na gudanar da shagulgulan kirsimetin. Yusuf Abdoulaye a Niaymey ya samu zantawa da wasu ga kuma rahotonsa.
Domin Kari