Yayin da wakoki na mawakan Afirka ke ci gaba da daukar hankali a duniya, da dama daga cikin masu fasahar waka a Najeriya na kallon wannan a matsayin wata dama ta yin suna da samun daukaka. Muryar Amurka ta zanta da DJ Cinch, wani mawaki mai tasowa a arewacin Najeriya wanda ke gauraya wakokin Afrobeats da Amapiano da gambara cikin Hausa.