A Ghana kuma, tun bayan bullar cutar Marburg mai hadari sosai a kasar, mutane a Kumasi da ke yankin Ashanti sun shiga cikin fargaba game da yiwuwar bazuwar cutar zuwa wurare da dama.
‘Yan uwan fasinjojin jirgin kasa da ‘yan bindiga ke ci gaba da garkuwa da su a arewacin Najeriya sun sake yin kira ga gwamnati da ta gaggauta kubutar da ‘yan uwan nasu, bayan wani bidiyo ya nuna yadda ake azabtar da su.
A jihar Kano dake arewacin Najeriya, jami’an tsaro sun kama wasu matasa wadanda aka zarga da daukan lokaci mai tsawo suna addabar al’umma da sace-sace, da fyade, da sauran ayyukan daba.
A birnin Kano na Najeriya, aikin Hajjin bana ya gamu da kalubale da dama da suka hada da rashin jigilar daruruwan maniyyata da kuma yadda aka taso keyar wasu maniyattan bayan sun isa Saudiya saboda yin amfani da biza ta bogi.
Malaman makarantu a Ghana sun janye yajin aikin makwanni biyu da suka yi da nufin matsa lamba ga gwamnati ta biya musu bukatarsu ta karin kashi 20 cikin 100 na albashi.
A wannan makon ne gwamnatin Najeriya ta kaddamar da fara aikin kamfanin man fetur na kasar a matsayin kamfani na ‘yan kasuwa mai hannun jarin gwamnati. Ana sa ran shigar ‘yan kasuwa cikin tafiyar da kamfanin na NNPC ta sa ya kara inganci da gudanar da ayyukanci cikin gaskiya.
Tarayyar Afirka ta ba da gudummawar kayan aiki na yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram na biliyoyin Naira ga sojojin rundunar hadin gwiwa da ke yaki da kungiyar a yankin tafkin Chadi. Ana sa ran sabbin motocin yaki, na na’urorin gano bama-bamai da aka dasa a karkashin kasa.
A Najeriya, a yayin da rashin tsaro ke ci gaba da ta'azzara a yankuna daban-daban ciki har da Abuja babban birnin kasar, masana harkokin tsaro na ganin amfani da bayanan sirri da kuma hadin kai tsakanin hukumomin tsaro a kasar shi ne kadai mafita.
Matasan suna wayar wa 'yannuwansu kai game da mallakar katunan zabe kamar yadda ya wakana a Jos, arewa ta tsakiyar Najeriya, wajen wani gangami na mallakar katin zabe.
Kungiyar likitoci na kasa da kasa (MSF) ta fara daukan matakai game da cututtukan da yara kanana ke fama da su a wannan lokaci na damina, wadanda suka hada da maleriya da kuma ta tamowa a yankin Damagaram na Jamhuriyar Nijar.
A bana, bukukuwan babbar Sallah da suka hada da yin yanka domin layya, na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke fama da matsalar tattalin arziki wakilyar Muryar Amurka Baraka Bashir ta ziyarci wasu kasuwannin Kano domin jin yadda farashin kayan abinci da tufafi da kuma dabbobi ya ke.
Iyalan likitan da mayakan ISWAP suka yi garkuwa da shi a Gubio a jihar Borno a watan Maris, sun yi kira ga gwamnati da ta yi duk mai yiwuwa don ganin an ceto shi. Matar likitan ta yi wannan kiran ne a wajen bikin ba da gidaje da kudi ga likitoci 81 a jihar da gwamnati ta yi.
Domin Kari