Wata kungiyar matasa a Jos, Rescue Frontier of Nigeria ta tashi tsaye domin ta wayar da kan mutane game da muhimmancin bayar da taimakon gaggawa. Kungiyar ta na ziyartar makarantu domin koyawa dalibai wasu dabarun agaji.
Ba kasafai ake samun mata Hausawa ke shiga wasannin motsa jiki ba, musamman wasannin Gymnastics wadanda ake amfani da lankwasa jiki da atisaye. Hakan kuwa saboda tasirin al'ada ce ta mutanen yankin. Sai dai wasu matan Hausawa a Abuja, sun shiga wannan wasa inda suke bukatar sauya wannan lamari.
A Jamhoriyar Nijar, masana a fannin kiwon lafiya sun bukaci jama’a, musanman wadanda ke Shirin yin aure, da su rika yin gwaji kafin aure, domin sanin irin rukunin jininsu, don rage hayayyafan yara masu sikila.
Kotun kolin Amurka ta yi fatali da hukuncin Roe v. Wade da aka kwashe shekaru da dama ana amfani da shi, wanda ya ba mata 'yancin zubar da ciki a kasar. Dama an sa ran kotun za ta yanke wannan hukunci, biyo bayan wani wani tonon silili a farkon wannan shekarar.
Dakarun Najeriya da ke yaki da kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin kasar sun ce ba za su huta ba har sai an kubutar da sauran 'yan matan Chibok da ke hannun kungiyar. Sojojin sun bayyana hakan ne a lokacin da suka gabatar da biyu daga cikin ‘yan matan.
Magungunan gargajiya su na bayar da muhimmiyar gudunmuwa a harkar kiwon lafiyar jama’a a Najeriya. Sai dai duk da muhimmancinsu, gwamnatoci ba su dauki matakin inganta sana’ar sayar da maganin gargajiya a kasar ba, lamarin da ya sa take cike da matsaloli.
Duk da samun munanan rikicin addini da kabilanci a jihar Filato a Najeriya, wata al’umma da ta yi kokarin ganin rikici bai iso gareta ba a duk shekarun nan, ita ce Mista Ali. Mun zanta da sarkin al’ummar akan yadda suka samu nasarar hakan.
Kwararru a fannin ilimi a Najeriya sun nuna bukatar gwamnati ta bunkasa bangaren ilimi na kasar, bayan ikirarin UNICEF akan cewa kashi 70 cikin 100 na yaran makaranta ba sa samun ilimi mai inganci.
Gwamnatin jihar Kano a Najeriya za ta bullo da sabbin matakai don kawo karshen yawaitar fashewar tukunyar gas daya kashe mutane da dama yayin da wasu sama da 50 suke kwance a asibiti bayan fashewar tukwanen gas a lokuta 4 cikin wata guda a jihar.
Masu kamfanoni da masana’antu a Najeriya suna kokawa da hauhawar farashin hatsi, musamman alkama, sakamakon yakin da Rasha ke yi da Ukraine.
Domin Kari