To mutane a fadin duniya dai na ci gaba da tsokaci a kan juyin mulkin da aka yi a Nijar, mun kuma samu jin ra’ayoyin wasu ‘yan kasar ta Nijar da kuma na wasu ‘yan Nijar mazauna Najeriya.
Mun duba wata hira ta musamman da Muryar Amurka ta yi da Shugaba Mohamed Bazoum a 2021, inda shugaban ya bayyana ra'ayinsa akan abinda ke kawo juyin mulki a wasu makwabtan kasar.
Akan wannan dambarwa dake faruwa a Nijar, mun samu tattaunawa da jakadan Nijar din anan Amurka, Mamadou Kiari Liman-Tinguiri.
A wani taron gaggawa da ta yi a Abuja a kan juyin mulkin a Nijar, kungiyar ECOWAS ta bai wa sojojin kasar wa’adin mako guda da su mayar da gwamnatin Mohamed Bazoum ko kuma ta dauki dukkan matakin da ya dace – wanda ya hada da yiwuwar amfani da karfin soji.
Sojojin da suka yi juyin mulkin a Nijar sun sanar da kwamandan sojojin dake gadin fadar shugaban kasar ta Nijar Abdourahmane Tchiani a matsayin jagoran gwamnatin kasar.
Duba tarihin juyin mulki a kasar Nijar, wannan dai shi ne karo na biyar da sojoji ke yin juyin mulki tun bayan da kasar ta samu ‘yancin kai daga Faransa a shekarar 1960
Mun tattauna da Aminu Mahi, wani ma’aikacin gwamnati a jihar Kanon Najeriyan don jin irin matakin da shi ma yake dauka a wannan lokaci da farashin mai ke gagarar wasu mutanen, da kuma tashin farashin kayan masarufi.
Matsalar rashin ishasshiyar wutar lantarki da Najeriya ke fama da ita, ta sa mutane da dama dogaro da janareta. Sai dai cire tallafin mai ya sa farashin man fetur ya haura, lamarin da ya sa 'yan Najeriya suke canzawa zuwa janareta mai amfani da iskar gas.
Mata 'yan wasan kwallon kafa a Afirka kamar takwarorinsu na Amurka ba a cika biyansu daidai da takwarorinsu maza ba. Kungiyar kwallon kafa ta mata t Super Falcons ita ce ta fi kowacce kngiyar kwallon mata a nahiyar Afirka samun nasara inda ta lashe kofuna tara a cikin goma sha daya na nahiyar
Mahalarta wani taron muhawara da Muryar Amurka ta shirya a Yamai babban birnin Nijar, sun shawarci shugabannin kasar da su dauki kwararan matakai domin rage dogaro akan kasashen ketare ta fannin abinci da makamashi.
Wasu daga cikin tambayoyin da mutane a Najeriya ke yi a game da shirin gwamnati na baiwa wasu ‘yan kasa kudi a kowanne wata, sannan wadanne ka’idoji za a duba wajen zabo mutane miliyan 12 da za su amfana da tallafin?
Kungiyar Taliban ta ba da umarnin rufe shagunan yin kwalliyar mata a cikin wata guda. Masu shagunan da masu fafutukar kare hakkin mata sun bayyana matakin a matsayin mummunan koma baya ga mata a kasar.
Domin Kari