Hukumomi da kungiyoyi a wajen Sudan su na hanzarin tsara shirye-shiryen kwashe kayayyakin tarihi da ake ta sace wa zuwa wuraren adanawa.
Nan da farkon shekara mai zuwa za a fara aiki da sabon tsarin biyan kudi na rage cinkoson ababen hawa a tsakiyar Manhattan na birnin New York a nan Amurka
Illolin matsalar wutar lantarki a Najeriya ba su tsaya kawai ga hana ci gaban tattalin arziki ba, har ma da bangaren kiwon lafiya.
Mun tattauna da Moustapha Kadi Oumani wani mai fafutukar ganin an wadata jama’a da lantarki a Nijar, a game da tasirin sabuwar tashar lantarki daga hasken rana.
Manoma a Ghana sun rungumi sabbin hanyoyin rage lalacewar kayan gonansu bayan girbi da kuma bunkasa hanyoyin samun kudaden shiga.
Shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum ya kaddamar da tashar samar da wutar lantarki mafi girma a kasar mai megawat 30, wanda zai kai ga gidaje 70,000, ko kuma mutane 500,000 a Yamai babban birnin kasar.
Hukumomin Ghana su na shirin kaddamar da wata tashar samar da wutar lantarki daga hasken rana da aka gina akan madatsar ruwa ta Bui, wadda za ta rika samar da lantarki mai karfin megawat biyar,
Basirar AI kamar ChatGPT suna zuwa da wasu sabbin matsaloli a fannin ilimi na Kenya, inda wasu daga cikin marubutan sun ce basirar AI ta na kawo musu cikas ga kasuwancin su, yayin da wasu farfesoshi ke nuna damuwa kan yadda basirar ta AI za ta bata dalibai, su koma yin cuwa-cuwa.
A makon da ya gabata ne Kotun Kolin Amurka ta yanke hukuncin hana amfani da tsarin ware wasu guraben daukan dalibai a jami’o’i bisa launin fatar dalibai.
Ana cewa karatu a jami’o’in gwamnatin tarayya a Najeriya kyauta ne, Malam Tijjani Mukaddasa ya mana karin haske game da dalilin da yasa jami’o’in ke bukatar dalibai su biya kudin rijista.
Karin kudin rijista sama da kashi 100 cikin 100 na wasu jami'o'in Najeriya ka iya tilastawa dalibai da dama barin karatu.
Ra’ayoyin wasu daliban Jami’ar Maiduguri a Najeriya kan yadda karin kudin makaranta zai shafi karatunsu.
Domin Kari