Wata kwararriya a Maiduguri, Dr Aida Abba Wajes ta yi karin haske akan illolin gurbatacciyar iska ga lafiyar mutane da kuma matakan da za a iya dauka.
An samu sarakuna biyu da kowannensu ke zaman fada a matsayin sarkin Kano a lokaci guda. Yayin da Muhammadu Sanusi da gwamnatin jihar ta mayar da ya rika karbar gaisuwa da mubaya’a a babban gidan sarautar, shi kuwa Aminu Ado Bayero, ya rika yin na shi zaman fada ne a gidan sarki dake Nasarawa GRA.
Farfesa Tijjani Naniya wani masanin tarihi a jami’ar Bayero dake Kano ya yi bayani kan inda dambarwar Kano ta samo asali.
Najeriya ce kasar da ta fi kowacce yawan matasa a duniya, inda kashi 70 cikin dari na mutanen kasar kamanin miliyan 207, matasa ne, kamar yadda bayanan kudin Worldometer suka nuna. Sai dai da rashin manufofi da suka dace da kuma tsadar kudin takara na hana matasa shiga siyasa.
A Afirka ta Kudu, rashin samun isasshen wakilci a siyasa da kuma yadda aka samu karin yawan masu kada kuri’a a zaben dake tafe, sun zaburar da matasan kasar shiga fagen siyasa.
‘Yar majalisar dokoki mafi karancin shekaru a Malawi, Fyness Magonjwa, ta shiga gaba wajen yaki da kalubalen da ke hana matasa shiga harkokin siyasa.‘Yar majalisar mai shekara 24 ta ce matasa su na fuskantar manyan kalubale idan suka so tsayawa takara duk da cewa matasa su suka fi yawa a kasar.
Cigaban tattaunawa da Farfesa Ahmed Adamu, masanin tattalin arziki a Najeriya kan yadda za a karfafa shigar matasa harkokin siyasa da shugabanci a Afirka
Natasha Mwansa ‘yar shekara 23 ta samu karbuwa a zukatan ‘yan Zambiya a 2014 lokacin da ta zo ta biyu wani shirin talabijin na kwaikwayon zaben shugaban kasa. Yayin da wasu ke kallon shirin a matsayin nishadi, a wurin Natasha, tamkar tsani ne na kaddamar da facutukarta ta neman shugabanci.
Farfesa Ahmed Adamu, wani masanin tattalin arziki a Najeriya, ya yi bayani kan abubuwan da suke kawowa matasa tarnaki a game da shiga siyasa da shugabanci a Afirka
Amurkawa da dama da za su yi zabe a watan Nuwamba, batutuwan da suka shafi Afirka ba su dame su sosai ba. Sai dai masu sharhi na ganin duk wanda ya yi nasara a zaben, yana da jan aiki na dawowa kimar Amurka a nahiyar ta Afirka.
Har yanzu matsalar cin hanci da rashawa ta na da girma sosai a kasashen nahiyar, ciki har da Ghana. A cewar hukumar kare hakkin dan Adam ta kasar, kashi 20 cikin dari na kasafin kudin kasar ya na silalewa ne saboda matsalar cin hanci da rashawa.
A kowacce shekara, dubban ‘yan Najeriya su na kai rahoton almundahana ga hukumomi. A 2021, kimanin korafe-korafe dubu 140 ne a ka shigar, wanda shi ne lamari mafi yawa a cikin shekaru hudu, a cewar hukumar ta EFCC.
Domin Kari