Ministan yada labarai na Najeriya, Mohammed Idris ya yi tsokaci a game da tasirin sashin Hausa na Muryar Amurka.
A ci gaba da shagulgulan cikar VOA Hausa shekara 45 da kafuwa, ma’aikatan shashin a Washinton DC sun gudanar da ‘yar kwarya-kwaryar liyafa, wacce ta samu halartar baki daga Amurka da wakilan ofishin jakadancin Najeriya a Washington.
Ministan Zongo a Ghana, Ben Abdallah Banda ya tsokaci a game da cikar Muryar Amurka shekara 45 da kafuwa.
A Yamai na jamhoriyar Nijar, Abdourahamane Mai Hula, wanda ya ke cikin masu sauraren sashin Hausa na Muryar Amurka tun lokacin da aka bude shashin shekaru 45 da suka gabata, ya yi tsokaci game da cikar Muryar Amurka shekara 45 da kafuwa.
Wasu matasa 50 masu kirkira kuma shugabanni daga kasashen Afirka 19 sun hallarci wani shiri na tsawon makonni 3 inda zasu samu horo kan shugabanci da kuma fannin bunkasa kwarewar su a babban birnin kasar Ghana, Accra ta hanyar shirin Young African Leaders Initiative ko kuma YALI a takaice.
Shugaban Amurka Joe Biden, a ranar Talata, ya ayyana kokarin gwamnatinsa na ganin an dakile sai da fentanyl da sinadaren da ake amfani da su wajen sarrafa mummunar kwayar bayan wata yarjejeniyar da aka kula da shugabannin China da Mexico a kwanan nan.
Batula Ali tayi fintikau inda ta kasance mace ta farko dake aikin tuka motar daukar marasa lafiya a sansanin ‘yan gudun hijira mafi girma na tuka dake Kenya.
Babban Darekta Janar mai kula hukumar da dakile yaduwar cutar ta AIDS NACA Gambo Aliyu, yayi bayani a game da ci gaban da hukumar ta samu a yakin ta da cutar SIDA a Najeriya da ma kalubalolin da ake fuskanta na kyamatar masu cutar.
Domin Kari