Shin wannan zanga-zanga da kungiyar NLC ta kira za ta sa al’amura su canja, kuma ko da gaske manufofin asusun lamuni na IMF da Bankin Duniya da Najeriya ke amfani da su, sun taimaka wajen shiga wannan yanayi? Wasu daga cikin tambayoyin da muka yiwa Dr Faruk Bibi Faruk kenan, malami a Jami’ar Abuja.
Wasu bidiyoyi da suka rika yawo a shafukan sada zumunta a farkon mako sun nuna yadda mutane dake zanga-zangar tsadar rayuwa a wasu wurare suka rika fasa runbunan abinci da tare motocin dakon abinci suna warwaso, abin dake nuna irin halin da ale ciki a kasar.
A jihar Borno a Najeriyar, halin matsin rayuwa ya sa mazauna garin Dikwa yin zanga-zanga, inda daruruwan mutane suka fito da nufin shiga daji don cin duk irin ganyen da suka ci karo da shi. Kazalika, mutanen garin sun ce yunwa na barazanar ingiza wasunsu shiga kungiyar Boko Haram.
Hukumomin Jamhuriyyar Nijar su na kokarin farfado da ayyukan yawon bude ido a kasar ta hanyar karfafa gwiwar mazauna kasar su rika ziyartar wuraren yawon bude ido da ake da su, a maimakon dogaro da baki ‘yan kasashen waje.
Kamfanonin aikin gine-gine a Zambia sun ce kamfanonin kasar China suna shiga cikin harkokinsu har ma suna karbe ayyukan da suka saba samu. Sun ce irin wannan gogayya ta tilasta wa wasu kamfanonin cikin gida a Zambiyar daina aiki.
Matsalar tsadar rayuwa sakamakon faduwar darajar Naira da ake ci gaba da fama da ita a kasar ta shafi bangarori da dama. A wannan rahoto da Baraka Bashir da aiko mana daga Kano, mun duba yadda matsalar ta shafi wasu marasa lafiya.
A jihar Kaduna dake arewacin kasar, wani mai fama da nakasa, ya na nunawa al’umma cewa ba duka aka zama daya ba, domin baya ga kama sana’ar yi, ya na kuma koya wa wasu masu nakasar sana’ar dogaro da kai.
Domin Kari