Masu kallonmu barkan ku da sake kasancewa tare da mu. Yanzu dai ‘yan kwanaki ne suka rage a gudanar da zaben shugaban kasar na Amurka. Tuni wasu daga cikin Amurkawa da ke zaune a kasashen waje suka kada ta su kuri’ar ta hanyar akwatin gidan waya.
Yayin da zaben shugaban kasa na ranar 7 ga watan Disamba a Ghana ke kara karatowa, wasu masu zabe a Kumasi suna cikin rashin tabbas a kan ko za su samu yin zaben, saboda rashin ganin sunayensu a rijistar zabe.
Duk da cewa tuni mutane da yawa suka kada kuri’arsu a zaben na Amurka, har yanzu Donald Trump na jam’iyyar Republican da Kamala Harris ta Democrat su na ci gaba da neman shawo kan Amurkawa da ba su yanke shawarar wanda za su kadawa kuri’a ba, wato Undecided Voters. Ga rahoton da Scott Stearns
A jihohin Florida, North Carolina, Georgia, ana ci gaba da fama da barnar da bala’in guguwa mai hade da ruwa ya yi, wanda ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane da janyo asarar dukiya ta biliyoyin dala. Muryar Amurka ta duba yadda ibtila’in zai yi tasiri wajen kada kuri'a a wadannan jihohin.
A zaben shugaban kasar Amurka, ba wai samun mafi yawan kuri’u ke da muhimmanci ba, a’a, muhimmin abu shi ne lashe mafi yawan kuri’un gundumomin zabe wato Electoral College, da ko wace jiha take da gwargwadon adadin nata. Ga yadda tsarin yake.
Domin Kari