Kasar Qatar ta dakatar da tattaunawar tsagaita bude wuta tsakanin Isra'ila da Hamas saboda abin da ta kira, rashin mayar da hankali daga bangarorin da ke fada da juna. A halin da ake ciki kuma, Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare a yankunan Gaza a kan Hamas da Hezbollah dake Lebanon.
Har haryanzu kasashen Afrika na ci gaba da bayyana ra’ayoyi da suka sha banban dangane da nasarar Donald Trump ta komawa fadar White House. Wasu na jin dadi da shaukin ganin abin da zai biyo baya, wasu kuma na tunawa da mulkin shi na farko.
A lokacin yakin neman zaben shi, Donald Trump ya yi alkawarin aiwatar da manyan abubuwa da suka hada da tsaron kan iyaka da karfafa tattalin arziki. Alkawuran na sa dai suna da girma, to amma ba a babu cikakkun bayanai kan yadda Trump din zai aiwatar da wadannan manufofi. Ga rohoton Tina Trinh.
Domin Kari