Bidiyoyin da al’amarin ya shafa basu kai kaso 1 cikin 100 na abubuwan da aka dora a kan dandalin ba a dan tsakanin da rahoton ya bayyana.
“Akwai bukatar APC ta fahimci cewa Najeriya kasa ce mai 'yancin kai kuma mulki yana hannun mutane.”
A wata sanarwa da kamfanin Dangote ya fitar ya ce ya sayarwa da kamfanin NNPCL da man fetur din da kudin dalar Amurka ba da Naira ba.
Taron zai gudana a birnin Legas dake Najeriya, daga ranar 10 zuwa 11 ga watan Satumbar da muke ciki.
Farashin man fetur na Talata ya kara fargabar karuwar hauhawar farashin kayayyaki A Najeriya. Wannan al’amari zai kara jawo wa 'yan kasa da 'yan kasuwa kunci mai tsanani.
Kungiyar masu masana’antu ta Najeriya MAN, ta ce karin kudin man fetur da aka yi zai iya haddasa tashin farashin kayayyaki a kasar.
Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta musanta ba kamfanin na NNPC umarnin ya kara farashin na litar mai.
Matatar man Dangote ta Najeriya ta fara sarrafa man fetur bayan tsaikon da aka samu sakamakon karancin danyen mai a baya-bayan nan, in ji wani jami'in gudanarwa a ranar Litinin kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito.
Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) ya tabbatar da cewa ya na fuskantar matsalar kudi sakamakon tsadar man fetur na manyan injuna (PMS), lamarin da ke kawo cikas ga dorewar ayyukan samar da man.
Hukumar da ke kula da gasa da kare muradun masu amfani kaya ta tarayya (FCCPC), ta ba da wa’adin wata guda ga ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki a kasuwannin da ke kara kazamin riba kan kaya da su rage tsadar farashin kayayyakin na su ko doka ta yi aiki kan su.
Rahoton na zuwa ne yayin da matsalar ambaliyar ruwa ta lalata amfanin gona da dama a wasu sassan kasar.
Domin Kari
No media source currently available
Bilkisu Nana Hassan, wata ma’aikaciyar gwamnati da ta yi ritaya a Kaduna, ta ce mata za su iya rungumar yin noma na zamani a cikin gidajensu, ba tare da sun je ko ina ba.